Connect with us

Labarai

Zazzabin Lassa na ci gaba da halaka mutane a Nijeriya

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce, an samu karin mutuwar mutane goma sha daya sakamakon cutar zazzabin Lassa.

A cewar cibiyar adadin ya nuna cewa, yanzu mutane dari da talatin da biyu ne suka mutu sanadiyar cutar ta Lassa.

Zazzabin Lassa ya barke a jihar Kaduna

Zamu fito da sabbin dabaru na yaki da cutar lassa- Ministan lafiya

 

Cibiyar ta kuma ce ko da yake an samu raguwar yaduwar cutar, amma duk da haka mutane tamanin da biyar ne suka kamu da cutar a makon jiya.

Cutar dai ta shafi kananan hukumomi Talatin a Jihohi tara na kasar nan wadanda suka hada da Edo da Ondo da kuma Ebonyi Sauran sune jihar Taraba da Kebbi da Filato da kuma jihar Kogi Cikin makwanni goma da suka gabata dai kasar nan ke ta fama da bullar cutar ta Lassa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!