Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ziyarar sabon Shugaban Civil Defence fadar sarki Kano

Published

on

Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, yayi kira da hakimai da dagatai da masu unguwanni dasu bawa sabon kwamandan hukumar Civil Defence hadin kai domin tabbatar da ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata’.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin daya karbar sabon kwamandan hukumar Civil Defence Muhammad Lawan Falala daya ziyarce shi a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace ‘aikin da hukumar Civil Defence takeyi yana da matukar mahimmanci wajen kula da rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar nan’.

A nasa jawabin sabon kwamandan hukumar Civil Defence din Muhammad Lawan Falala yace ‘ya ziyarci masarautar Kano ne domin Neman hadin Kan masarautar, tare da samun goyon bayan ta wajen gudanar da aikinsa ka’in da na’in a jihar kano’.

Sabon kwamandan yana tare da dukkanin manyan jami’ansa a yayin da ya Kai wannan ziyara.

Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!