Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kano na nema wasu mutane 16 ruwa a jallo

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana mutum 9 daga cikin mutane 16 da ake zargi da aikata daba a jihar a matsayin wadanda ta ke nema ruwa a jallo.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumal ne ya bayyana hakan, yayin taron masu ruwa da tsaki kan tsaro da ya gudana a karamar hukumar Dala.

CP Muhammad Usaini Gumal ya Kuma ce ‘daga cikin mutanan data gayya 16 mutum 7 ne suka Kai kan su gareta, Inda suka tabbatar mata da daina duk wasu abubuwa da suka danganci Daba a jihar ta Kano’.

Kwamishinan ‘yan sandan na Kano Muhammad Usaini Gumal ya Kuma ce, ‘Talauci da matsan rayuwar da ake ciki a halin yanzu ne ke sanyawa da yawan matasa aikata ayyukan ta’addanci’.

Rahoton: Aminu Abdu Baka Noma

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!