Labarai
Ziyarar ta’aziyya: Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zo Kano
Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci jihar Kano domin yin ta’aziyyar ɗalibar nan Hanifa Abubakar da ake zargin malamainta da kashe ta.
Mataimakin shugaban ya iso Kano tare da tawagarsa inda kuma ya ziyarci gidan su ɗalibar da ke unguwar Dakata domin yin ta’aziyya.
Mataimakin shigaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya buƙaci iyayen ɗalibar nan Hanifa Abubakar da ake zargin malaminta ya kashe ta da su dauki batun a matsayin kaddara.
Farfesa Yemi Osibanjo ya kai ziyarar gidan iyayen marigayiyar karkashin jagorancin gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagorance shi.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana rasuwar dalibar a matsayin babban rashi baga iyayen ta kadai ba har ma da kasar nan baki daya.
Har ma ya ce, gwamnatin tarayya ta kadu da jin labarin kisan dalibar wadda ake zargin malamin ta da yin garkuwa da ita da kuma kashe ta.
Wakilyar Freedom Radio Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar ya kai ziyarar ta’aziyyar ne a wani bangare na halartar taron kungiyar malaman lauyoyi karo na 53.
You must be logged in to post a comment Login