Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Soji: an fitar da sunayen wadanda suka samu nasarar shiga aikin soji (short service)

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta fitar da jerin sunayen wadanda suka samu nasarar neman gurbin shiga aikin kananan hafsoshin soji wato (short service) na wannan shekara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau juma’a.

Sanarwar ta ce, wadanda suka samu nasarar ana bukatar da su je jami’ar soji da ke Kaduna wato (NDA) a ranar shida ga watan gobe na Afrilu, inda za a horar da su na gajeren zango.

Haka zalika a cewar sanarwar, ana bukatar wadanda suka samu nasarar da su je da takardun makarantunsu na ainihi da kuma kwafin rajistar da su ka yi ta kafar internet wanda ke dauke da hotunan su.

Sauran kayayyakin da ake son su je da su, sune: karamin hoto mai kala guda hudu wanda kuma ba a dauke shi da hula ba, bakaken wanduna guda biyu, da takalmi canvas guda biyu da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!