Labarai
Zuwa 2020 Najeriya zata fara hada motocin masu amfani da hasken rana
A yayin da Najeriya ke bikin samun ‘yancin kai karo na 59 wani kamfanin hada motoci ya sha alwashin karfafa kokarinsa na ganin ya fara hada motocin da suke amfani da hasken rana a nan da shekara ta 2020.
Shugaban kamfanin, Sun Energy Development Initiatives Mr Moses Onaga ne ya bayyana haka a jiya yayin bikin samun yancin kai da aka gudanar, a wani taron baje kolin kayayyakin da ke amfani da hasken rana a garin Ibadan.
Kamfanin dilanci labarai na kasa NAN ya rawaito cewar baje kolin an shirya shi ne domin karfafawa yan Najeriya gwiwa wajen samun makamashi da bashi da illa ga muhalli.
Ya kara da cewa, baje kolin wani yunkuri ne na tabbatar da ‘yan Najeriya sun fara amfani da kayan masafurin da basu da illa ga muhalli a kokarin samun Najeriya mai tsafta da inganta lafiya.
Mr Moses ya ce babban burin masu rajin kare muhalli shine tabbatar da Najeriya ta fara hada motoci da basa gurbata muhalli, tare da rage yawan amfani da kayayyakin kasar