Hukumae EFCC ta rufe asusun ajiyar banki guda talatin mallakar tsuhuwar shugaban hukumar inshora

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta rufe asusun ajiyar banki guda talatin mallakin tsohuwar shugabar hukumar inshorar lafiya ta kasa Dr. Ngozi Olojeme.

 

Haka zalika hukumar ta EFCC ta kuma karbe iko da wasu kadarori guda talatin da bakwai mallakin Dr. Ngozi Olojeme.

 

Hakan ya biyo bayan wani umurni da wata babbar kotun tarayya ta bayar, wadda ta bukaci EFCC da ta kwace iko da kadarorin da kuma rufe asusun ajiya na bankunan.

 

Rahotanni sun ce a daya daga cikin gidaje talatin da bakwai da hukumar EFCC ta kwace da ke lamba 25 kan titin Kainji Crescent a unguwar Maitama da ke birnin tarayya Abuja, yana dauke da ban daki na sarakai wanda akayi kiyatsin cewa an kashe dala miliyan biyu zuwa dala miliyan hudu wajen kawata bandakin da kayan alatu.

 

A watan Janairun daya gabata ne hukumar EFCC ta gurfanar da Dr. Ngozi Olojeme gaban kotu bisa ga zarginta da almundahanar sama da naira biliyan sittin da biyu.

The short URL of the present article is: http://freedomradionig.com/default/frbJXtq

Opinion Polls

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO