Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

jami’an hukumar DSS sun kama tsohon Gwamnan Benue Gabriel Suswam

Published

on

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke tsohon Gwamnan jihar Benue Gabriel Suswam, sakamakon wata matsalar tsaro da ta kunno kai.

Hukumar ta cafke tsohon Gwamnan ne bayan da Gwamnan jihar na yanzu Samuel Ortom ya shigar da korafi gaban hukumar ta DSS yana mai zargin tsohon Gwamnan do kokarin yiwa al’amuran tsaro karan tsaye a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar bara ne hukumar ta DSS ta cafke tsohon Gwamnan jihar ta Benue, bayan da ta bankado wasu manyan makamai da ake zargin mallakin Gabriel Suswam din ne.

Wata Majiya mai karfi ta tabbatar da cafke tsohon Gwamnan da hukumar DSS din tayi biyo bayan shigar da korafi da Gwamnan jihar yayi gaban ta.

Wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin ta Tony Opuiyo  ta ruwaito cewa an samu makaman ne a shekarar bara a yankin Aguiyi Ironsi da ke Maitama a birnin tarayya Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!