Labarai
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana kaɗuwa bisa rasuwar tsohon shugaban Ƙasa Buhari

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa NSGF ta bayyana kaɗuwa da alhininta game da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, tana mai cewa wannan babban rashi ne ba wai ga Arewa kadai ba, har da kasa baki ɗaya.
Wannan na cikin sanarwar da Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar Inuwa Yahaya, marigayin tsohon shugaban ƙasa Buhari mutum ne da rayuwarsa ta ƙunshi ladabi, rikon gaskiya da ƙwazo wajen hidima ga ƙasa tun daga lokacin da ya fara aiki a matsayin matashin soja, har zuwa shugabancinsa na mulkin soja da na dimokuraɗiyya.
You must be logged in to post a comment Login