Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun ƙone gidan shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara  

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun ƙone gidan shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya a ƙaramar hukumar Zurmi.

Shugaban kwamitin harkokin tsaro na majalisar Alhaji Abdullahi Shinkafi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar sa, ƴan bindigar sun shiga yankin ne tare da cinnawa gidaje wuta ciki har da gidan shugaban majalisar.

A cewar sa, harin nasu ya zo ne sakamakon yadda sojoji suka buɗe musu wuta a ƴan kwanakin nan musamman ma a yankin na Zurmi.

Shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Shinkafi bai yi ƙarin haske kan ko an rasa rayuka sanadiyyar wutar  ba, amma ya ce tuni gwamnatin jihar ta bada umarnin akai ɗaukin gaggawa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!