Connect with us

Labarai

Ƴan sanda sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Zamfara

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta ce ta kuɓutar da wani mutum da masu garkuwa da mutane suka sace a ƙauyen Sabon garin Rini.

Mai magana da yawun rundunar Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai a ranar Talata.

Gambo ya ce masu garkuwar sun kama Mudassir Malam ne a Kauyen Sabon garin Rini da ke Karamar hukumar Bakura inda ya kwashe sati shida yana tsare a hannunsu.

Ya ƙara da cewa jami’an rundunar sun sami nasarar kuɓutarda Malam ne tare da haɗin gwiwar jami’an sa kai na Vigilante na yankuna daban daban da sauran jami’an tsaro ba tare da ya sami wani rauni ba.

Yanzu haka dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Ayuba El-Kanah ya miƙa Mudassir ga shugabancin ƙaramar hukumar ta Bakura domin sadashi da iyalansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!