Connect with us

Labarai

Ƴan sandan Kano sun kama mutane 33 da ake zargi da aikata Daba

Published

on

Rundunar  Ƴan sandan Jihar Kano, ta kama mutane 33 da ta ke zargin su da aikata ayyukan daba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ruwaito cewa, rundunar ta cafke matasan ne yayin wani aikin sintirin da ta gudanar na tsawon kwanaki biyar domin kakkaɓe masu aikata mummunan aiki a cikin birnin Kano.

Haka kuma ta bayyana cewa an kama mutanen ne tsakanin ranakun 23  zuwa 28 ga watan nan da muke ciki na Afrilu a wuraren da aka gano cewa ɓata garin na aikata masha’ar su.

SP Kiyawa, ya kuma bayyana cewa, an gudanar da aikin ne ta hannun jami’ai na musamman da ke ƙarƙashin jagorancin kwamishinan Yan sandan Kano CP Ibrahim Bakori, da kuma shugabancin CSP Bashir Gwadabe na sashen yaƙi da ayyukan daba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!