Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An samu raguwar fadan daba a Kano Yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce, yanzu haka an samu raguwar ayyukan fadan Daba da kuma kwacen Wayoyin mutane a fadin jihar sakamakon sabbin dabarun da ta bullo da su.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

SP Kiyawa ya ce, daga cikin dabarun da rundunar ta bullo da su, akwai yin yafiya ga masu aikata laifi matukar suka tuba tare da mika wuya ga rundunar da kuma shirya wasannin Kwallon kafa a tsakanin tubabbun.

Haka kuma Rundunar ta ce yanzu haka an kwashe tsawon kwanaki da dama rundunar ba ta samu rahoton masu aikata Kwacen Wayoyin mutane da kuma ayyukan fadan Daba ba a fadin jihar Kano.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!