Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ɓaraka ta ɗinke a APCn Kano – Abdullahi Abbas

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya ce an ɗinke ɓarakar da ta kunno a jam’iyyar.

A wani saƙon murya da Freedom Radio ta samu, shugaban ya ce Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci sasanta rikicin da ya kunno a APCn.

A makon da ya gabata ne rikici ya ɓarke tsakanin shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa da Mataimakin ɗan takarar Gwamnan APC Murtala Sule Garo.

Sai dai Abdullahi Abbas ya ce, yanzu an yi maslaha kowa ya yafewa kowa.

Shugaban ya yi kira ga sojojin baka da ƴan social media kan su ci gaba da bai wa jam’iyyar haɗin kai.

A ranar Lahadi ne jam’iyyar APC ta gudanar da taron masu ruwa da tsakinta kan wannan rikici a fadar Gwamnatin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!