Kasuwanci
Ƙarancin mai duk ƙasa ne ba iya Kano ba – Ɗan Malam
Ƙungiyar dillalan Man Fetur ta ƙasa IPMAN reshen jihar Kano ta gargaɗi mutanen da suke sayan man Fetur su ajiye a gida.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Bashir Ɗan Malam ne ya bayyana hakan, a daren Litinin yayin da ya amsa gayyatar da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano ta yi masa.
Ɗan Malam ya ce, ajiye man Fetur a gida ganganci ne da zai iya zama hatsari ga jama’a.
Dangane da ƙarancin man kuwa Ɗan Malam ya ce, dama tun a baya sun yi gargaɗin cewa za a iya shiga wannan matsala, sakamakon yadda defo-defo ɗin man suka tsaya.
Ya ci gaba da cewa, matsalar ƙarancin mai ba iya Kano ba ce kaɗai, matsala ce da ta shafi ƙasa baki ɗaya.
A nasa ɓangaren shugaban hukumar Anti Kwarafshin Barista Mahmud Balarabe ya ce, sun gayyaci shugaban IPMAN saboda yadda jama’a suke ta yin ƙorafi kan matsalar ƙarancin man fetur.
Barista Balarabe ya ce, sun tattauna har tsawon awanni 3 da Ɗan Malam kuma yayi gamsashshen bayani.
Ya ƙara da cewa, a yanzu an fitar da tirela 88 domin rarraba wa ga gidajen mai a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login