Labarai
Ƙudurin dokar ƙwarya-ƙwaryan kasafin bana ya tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano
Ƙudurin dokar ƙwarya-ƙwaryan kasafin bana na fiye da Naira biliyan 58 da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar, ya tsallake karatu na biyu a zauren.
Ƙudurin, ya cimma wannan nasara ne a zama na musamman da majalisar ta gudanar yau Alhamis.
Yayin zaman, shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya gabatar da karatun na biyu inda kuma mambobin majalisar suka amince da shi.
Majalisar ta miƙa aikin taza da tsifa na ƙudurin ga shugaban kwamitin harkokin kasafi zauren Aminu Sa’adu mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo tare da bai wa kwamitin mako guda domin ya gabatar da rahotonsa.
Haka kuma yayin zaman na yau, majalisar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta gina titi a hanyar da ta tashi daga garin Kwankwaso ta bi ta Kanwa zuwa garin Ƙauran Mata.
Buƙatar dai ta biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Madobi a zauren Sulaiman Mukhtar Ishaq ta gabatar wanda shi ma ya samu amincewar wakilan majalisar.
Shi ma dai wakilin ƙaramar hukumar Gezawa Abdullahi Yahaya, ta gabatar da ƙudurin neman gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta gina titi a hanyar da ta tashi daga Babban titin Hotoro Eastern bypass ta bi ta garin Jar Kuka da Rabawa Gidan Kwano har zuwa garin Gunduwawa da ke kan titin zuwa Hadejia.
You must be logged in to post a comment Login