Labarai
Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta shirya tsunduma yajin aiki
Biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan bukatunta, kungiyar likitocin Nijeriya masu neman ƙwarewa NARD ta shirya fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar daga karfe 8:00 na safe a ranar Laraba 17 ga watan Mayu zuwa karfe 8:00 na safen Litinin 22 ga watan nan da muke ciki na Mayu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Likitocin a ranar 29 ga Afrilu, sun ba da wa’adin makonni biyu ga gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu ko kuma su dauki matakin gaggawa wanda Kuma wa’adin ya ƙare a ranar Asabar, 13 Mayu.
Shugaban Kungiyar likitocin ta NARD, Dakta Emeka Innocent Orji, ya shaida wa manema labarai cewa, idan gwamnati ta gaza mayar da martani kan wannan batu bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar, ba su da wani zabi da ya wuce su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Ya ce abin da aka samu daga taron shi ne mambobinmu a duk fadin kasar nan sun ba mu ikon ayyana yajin aikin gaba daya , Yajin aikin dai zai fara ne daga ranar Larabar wannan mako na tsawon kwanaki biyar, inda daga nan ne za mu duba lamarin.
Ya jaddada cewar idan gwamnati ba za ta mayar da martani ga dukkan batutuwan da muka lissafo ba, babu shakka zamu tsunduma yajin aikin gama-gari .
You must be logged in to post a comment Login