Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shiga yajin aikin NARD ya saba doka- Gwamantin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bayyana yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta fara a matsayin abin da ya saba wa doka.

Mai magana da yawun ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi ta tarayya Olajide Oshundun ne ya sanar da hakan ranar Talata a tattaunawarsa da Jaridar Daily Trust, bayan karbar wasikar kungiyar likitocin.

Olajide Oshundun, ya ce, kungiyar ba ta cika ka’idar wa’adin makonni ukun da ya kamata a ce likitocin sun bayar kafin fara yajin aikin ba, kasancewar ranar 15 ga watan Mayun nan suka rubuta wasikar.

Daga cikin bukatun kungiyar ta likitoci masu neman kwarewa akwai batun inganta albashi da alawus, da biyan kudaden ariya na albashi, da kudin horo da sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!