Kiwon Lafiya
Ƙungiyar NARD ta janye yajin aikin da ta shafe sama da watanni 2 tana yi
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa NARD ta janye yajin aikin da ta shafe sama da watanni biyu tana yi.
Ƙungiyar ta kuma ce a shirye ta ke ta koma aiki a ranar Laraba mai zuwa domin ci gaba da gudanar da ayyukan ta.
Shugaban ƙungiyar Godiya Ishaya ne ya tabbatar da hakan a safiyar Litinin ɗin nan a Abuja.
Ya ce, janye yajin aikin ya biyo bayan ganawar da suka yi da ƙungiyar likitoci NMA jiya Lahadi inda ta buƙace su da su janye yajin aikin nasu.
Tun a jiya Lahadi ne ƙungiyar ta NARD ta bayyana cewa za ta janye yajin aikin da ake, ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakatarenta Ekpe Philips Uche ya fitar, jim kaɗan bayan kammala taro da shugabannin kungiyar NMA a Abuja.
A jawabin shugaban ƙungiyar NARD Godiya Ishaya da safiyar yau Litinin ya tabbatar da cewa za su koma bakin aiki a ranar Laraba mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login