Labarai
Ƴan Chana ne suka kawo matsalar tsadar Kaya: MARTAN
Hana ƴan chana shigowa kasuwanci a jihar Kano shine zai habbaka kasuwanci a jihar KanoG
Gamayyar kungiyoyin ƴan kasuwar ƙasar nan reshen jihar Kano ta ce hana ƴan ƙasar Sin Chana shigowa kasuwar kwari shi zai taimaka wajen samar da tsayayyen farashi a harkar kasuwancin su
Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban ƙungiyar reshen Kano Alhaji Auwal Illiyasu yayin da yake zantawa da manema labarai kan yadda ake samin ƙaruwar farashi a cikin kasuwar kwari
Auwal ya kuma ce yadda ƴan Sin suke shigowa cikin kasuwar kwari suna ganin yadda ƴan kasuwa suke shiyar da kaya ya sanya suma suke sake ƙara farashi wanda hakan ya sanya kullum idan sukaje saro kaya yakan ƙara tashi
Haka kuma sun samar da yara a cikin kasuwar ta kwari domin zuwa suna zagayawa domin jiyo musu yadda ƴan kasuwar suke shiyar da kayan da suka shiya daga hannun ƴan Chana
Sai ƴan kasuwar na kira ga gwamnati da ta dakatar da ƴan Sin Chana daga shigowa kasuwannin Kano wanda hakan zai daidaita farashin kaya a kasuwar
You must be logged in to post a comment Login