Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ya kamata iyaye su rika kai ‘ya’yansu alluran Riga-kafi- NMA

Published

on

Kungiyar Likitocin Nijeriya NMA, ta bukaci, Iyaye da su tabbatar da sun yi wa ‘ya’yan su ‘yan kasa da shekaru biyar alluran riga kafin kamuwa da cutuka.

Shugaban kungiyar shiyyar Kano, Dakta Abdullahi Kabir Sulaiman ne ya bukaci hakan yayin da kungiyar ke gudanar da bikin makon Likitoci na bana.

Dakta Abdullahi Kabir Sulaiman ya kuma ce, a wannan lokaci da ake ciki ya zama wajibi gwamnati ta rika fitar da kaso mai yawa na kasafin kudinta a fannin lafiya duba da karuwar bullar cutuka da ake samu.

Ya kara da cewa a Jibi Laraba ne kungiyar za ta gabatar da aikin duba marasa lafiya kyauta a babban asibitin karamar hukumar Kiru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!