Labarai
Ƴan Najeriya dubu ɗari 330 ne suka yi gudun hijra zuwa wasu ƙasashen – Sadiya Umar
Gwamnatin tarayya ta ce, yan Najeriya sama da dubu dari uku da talatin ne ke zaune a kasashen da ke makwabtaka da kasar nan sakamakon ayyukan yan bindiga a yankin Arewa maso Gabas da Arewa masu Yamma.
Ministar jin kai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan a wani taro da ya mayar da hankali kan matsalolin ci gaban al’umma da karancin abinci a kasar nan.
Sadiya Umar ta ce, a yanzu adadin yan Najeriya da suka yi gudun hijra zuwa yankin Chadi sun kai dubu goma sha shida da dari shida da talatin da hudu.
Yayin da wadanda suke Kamaru sun kai dubu dari da goma sha takwas da dari hudu da tara, sai wadanda suke a jamhuriyar Nijar da yawan su ya kai dubu dari da tamanin da shida, da dari tara da hamsin da bakwai.
Ministar ta bayyana fargabar ta kan yadda karancin abinci ya shafi mutane miliyan uku da dubu dari hudu, a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, sai kuma mutane miliyan hudu da dubu dari uku ke tsamannin tallafin abinci daga wajen gwamnati a yanzu haka.
You must be logged in to post a comment Login