Labarai
Ƴan Najeriya dubu 76 ne aka kashe cikin shekaru 10 da suka gabata – Gwamnoni.
Ƙungiyar gwamnonin ƙasar nan ta ce tsakanin watan Mayun shekarar dubu biyu da goma sha ɗaya zuwa Fabrairun wannan shekara, sama da ƴan Najeriya dubu saba’in da shida ne suka rasa rayukansu sanadiyar ayyukan ƴan tarzoma a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin na Najeriya Kayode Fayemi na jihar Ekiti shine ya bayyana haka a jiya lokacin da ya ke ƙaddamar da wani shirin tsaro da ƙungiyar ta gabatar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, ba ya ga kwararar ƙananan makamai zuwa ƙasar nan ba bisa ƙa’ida ba, wadda sanadiyar hakan ta janyo rikice-rikice na ƙabilanci da ta’addanci, al’amura da dama sun sukurkuce sanadiyar hakan.
Gwamnan jihar na Ekiti ya kuma ce matsalar rashin tsaron na ci gaba da kawo tarnaki ga ci gaban ƙasar nan
You must be logged in to post a comment Login