Labarai
Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 5 a harin Rabah
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ta tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da kona kayan abinci da abubuwan hawa, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai da safiyar Litinin din makon nan a garin Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.
Mai magana da yawun rundunar a jihar ASP Ahmad Rufa’i, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.
Jami’in ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne inda suka harbe mutane biyar, da kuma kona kayan abinci da babura da motoci, kafin daga baya jami’an tsaro na hadin gwiwa su kai dauki yankin.
A baya dai an samu makamancin wannan hari a garin Duhuwa na karamar hukumar Wurno da ke kusa da Rabah duk a jihar ta Sokoto da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama.
You must be logged in to post a comment Login