Ƙetare
Ƴan ta’addan ISWAP sun kai hari sansanonin Soji a Kamaru

Rahotanni daga Arewa maso Gabashin Najeriya, sun nuna cewa, ƴan ta’addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a garuruwan Banki da Freetown da ke kusa da iyakar Kamaru, inda mutane sama da dubu biyar suka tsere zuwa cikin Kamaru.
Rahotonni sun bayyana cewa, maharan sun yi yunkurin mamaye sansanin sojojin ne cikin dare, sai dai bayan musayar wuta tare da samun dauki daga sojojin sama, aka fatattake su, inda sojoji biyu da fararen hula bityu suka rasa rayukansu tare da lalata gidaje da dama.
Harin ya biyo bayan farmakin da aka kai Darul Jamal makonni biyu da suka gabata, inda aka kashe mutane kusan 90.
Duk da raguwar tashin hankali tun bayan shekarun 2013 zuwa 2015, rikicin Boko Haram da ISWAP ya ci gaba da addabar arewa maso gabashin kasar nan, inda ya hallaka fiye da mutane 40,000 tare da tilasta sama da miliyan biyu barin gidajensu tun 2009.
You must be logged in to post a comment Login