Labarai
Ƴan wasa da jami’ai 6,382 ne suka yi rijista a gasar Matasa ta bana

Hukumar wasanni ta kasa NSC, ta tabbatar da cewar ‘yan wasa da masu horar da su 6,382 suka halarci gasar matasa ta kasa karo ta 9 da zata gudana Asaba babban birnin jihar Delta.
Jawabin na hukumar ya biyo bayan kammala yin rijista da akayi na jahohi 36, ciki harda birnin tarayya Abuja.
Hukumar tace samun karuwar masu halartar gasar na da alaka da yadda gasar ke kara bunkasa tare da samar da kwararrun matasan ‘yan wasa.
‘Yan wasa 4,961 da masu horar dasu 386 da manajoji su 400 da suka fito daga jahohin kasar nan daban daban, ne yanzu haka suka halarci gasar.
Za a fafata wasannin 37 da suka hada da wasan kwallon kafa da kwallon Raga da kwallon kwando, sai kwallon yashi da kwallon zari Ruga da sauran su daga cikin wasanni 9 da za’ayi na kungiyoyi.
Haka zalika akwai wasannin da suka kunshi mutane bibiyu ko mutun guda da irin su suka hada da tsere na gudu da lunkaya da kokawar ta zamani da ta gargajiya da tseran Keke da jefa abu mai nauyi da Damben zamani.
Jahar Delta wadda itace a kan gaba wajan zama ta daya, a wannan karon zata iya fuskantar kalubale a wajan jahohi irin su Ogun da Lagos da River kana Edo.
Tuni dai aka tantance ‘yan wasa a Alhamis 28 ga Agusta kana a gobe Jumma’a 29 ga watan za’a bude gasar, a hukumance, wacce za a Kammala ta a ranar Asabar 6 ga Satumba.
You must be logged in to post a comment Login