Labarai
Ƴancin kai: Najeriya na cikin jerin ƙasashen da aka bari a baya – Tanko Yakasai
Wani tsohon dan siyasa anan Kano ya bayyana cewa har yanzu Najeriya na cikin jerin ƙasashen da aka bari a baya musamman ta fannin ci gaba.
Alhaji Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan jim ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radiyo, wanda yayi duba kan bikin cika shekara 61 da samun yancin kan Najeriya.
Alhaji Tanko Yakasai ya ce, akwai kasashe da suka samu ƴanci tare da kasar nan amma a yanzu kasashen sun yiwa Najeriya fitinkau.
“Idan muka yi duba a ɓangaren ilimi za mu ga cewa tuni ɓangaren ya samu koma baya, ta yadda a yaznu mun gwammace mu tura yaran mu ƙasashen duniya don siyo karatu sama da mi inganta makarantun ƙasar ma” in ji Yakasai.
Alhaji Tanko ya kuma ce “Rungumar tsarin noma ita ce hanya ɗaya da za a magance matsalar tattalin arziƙi da kuma barazanar tsaron da ake fuskanat, domin kuwa duk wanda ya samu aikin yi ba zai sanya kan sa a mummunar ɗabi’a ba”.
You must be logged in to post a comment Login