Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina Salihu Yakasai ya ke?

Published

on

An wayi gari Asabar da samun rahoto daga makusantan Salihu Tanko Yakasai kan cewa bai dawo gida ba tun a ranar Juma’a.

Hakan kuma ya zo ne bayan da ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter da a ciki ya bayyana gazawar Gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, mahaifinsa Alhaji Tanko Yakasai ya ce, jami’an tsaro ne suka cafke shi.

To amma amma hukumar tsaron DSS ta ce, ba ita ta cafke shi ba.

Labarai masu alaka:

Ina Salihu Yakasai ya ke?

Dalilan da suka sanya Ganduje ya dawo da Salihu Tanko kan mukaminsa

Jaridar Daily Post ta rawaito shugaban hukumar tsaron farin kayan shiyyar Kano Muhammad Alhassan na cewa, ko gayyatar Salihun ba su yi ba, balantana su kama shi.

Ko da Freedom Radio ta tuntuɓi shugaban hukumar ya ce, bai san komai ba game da lamarin.

Freedom Radio ta tuntuɓi sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kano Malam Abba Anwar sai dai ya ce, ba a bashi izni ya yi magana kan batun ba.

Yanzu haka dai ƴan Najeriya da dama ne suka shiga yin kiraye-kiraye kan ɓatan Salihun musamman a kafafen sada zumunta.

Ga wasu daga ciki:

I just recieved a news of incarseration of my very good friend Salihu Tanko Yakasai AKA Dawisu, Special Adviser to the…

Posted by Bashar Ummarun Kwabo on Saturday, February 27, 2021

Now that it was confirmed Dawisu is at DSS office, Is he a bandit or a terrorist? What was the reason for his arrest? ☕️

Posted by Amina Muhammad on Saturday, February 27, 2021

Allah sarki mu. Ahe duk sukar da muka rika yi wa Manjo a da asiri aka yi mana😭😭 Ni dai na san a irin adalcin hukumar DSS bata kama mutumin da asiri ya sa shi aika-aika. #FreeDawisu

Posted by Abdulaziz Tijjani on Saturday, February 27, 2021

 

Waye Salihu Yakasai?

Shi ne mai taimaka wa Gwamnan Kano kan yaɗa labarai, fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta ne da lokaci zuwa lokaci ake damawa da shi a siyasar kafafen sada zumunta.

A shekarun baya dai yana cikin waɗanda ke kare muradan Gwamnatin jam’iyyar APC tare da yin raddi ga duk wanda ya saɓa mata.

A watannin baya ma dai Gwamnan Kano ya dakatar da shi daga muƙaminsa bayan da ya soki tsarin gudanarwar Gwamnatin tarayya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!