Labarai
Ɓatan kuɗaɗen marayu: An dakatar da manyan jami’an kotunan Shari’ar Muslunci na Kano
Hukumar ɗauka da ladabtar da ma’aikatan shari’a ta Kano ta dakatar da Akanta da Daraktan Kuɗi na kotunan Shari’ar Muslunci na jihar.
Hukumar ƙarƙashin Babban Jojin jiha Mai Shari’a Nura Sagir Umar ta sanar da dakatarwar ne a yau Litinin.
An dakatar da manyan ma’aikatan biyu ne sakamakon zargin badaƙalar ɓatan kuɗaɗen marayu har miliyan 345 daga asusun kotunan Muslunci.
Mai magana da yawun kotunan Kano Baba Jibo Ibrahim ya shaida wa Freedom Radio cewa, an dakatar da ma’aikatan har zuwa kammala bincike.
Idan zaku iya tunawa a ranar 13 ga watan Satumban da muke ciki ne, Freedom Radio ta bankaɗo badaƙalar ɓatan kuɗaɗen.
Ita ma hukumar yaƙi da rashawa ta Kano PCACC ta ce, tana bincike a kan ɓatan kuɗaɗen.
You must be logged in to post a comment Login