Manyan Labarai
2023: Gadar Ganduje a APC Barau ko Gawuna?
Bayan kammala zaben shekarar 2019 ne wasu gwamnonin kasar nan zasu kammala wa’adin su akan karagar mulki kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanadar musu.
Daga cikin wadannan Gwamnoni da ake sa ran zasu kammala mulkin su zango na biyu a shekarar 2023 akwai gwamnan Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Daga ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023 tayi ana sa ran Gwamna Ganduje zai mika ragamar mulkin jihar Kano ga duk wanda Allah madaukakin sarki ya zaba.
Amma duk da haka ita kujerar gwamnan jihar Kano kujera ce da manya da kananan ‘’yan siyasa ke zawarcinta sakamakon tagomashi da kujerar ta gwamnan Kano take da shi tun sanda aka kirkiri jihar a ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 1967.
Tun dawowa Najeriya mulkin dumkradiyya a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne mutum na uku da ya samu damar mulkar jihar Kano a tsarin na dumkradiyya.
A zaben shekarar 2015 tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya tsayar da tsohon mataimakin sa Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi daga tsagin Kwankwasiyya.
Dr Abdulllahi Umar Ganduje yayi nasarar zama Gwamnan Jihar ta Kano a zaben ranar 11 ga watan Afrilu na shekarar ta 2015 daga bisani Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya mika masa mulki a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar ta 2015.
Tun baa je koina ba sai dangantaka tayi tsami tsakanin aminan siyasar guda biyu sakamakon zargin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje tayiwa tshon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da rashin ladabi lokacin da yazo yin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje wacce Allah yayiwa rasuwa a watan Maris na shekarar 2019.
Wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa shi ne ya sa tsohon gwamnan na Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya tattara ya nasa ya nasa shi da mukarrabansa suka yi hijira zuwa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP.
An shiga zaben shekarar 2019 inda a zagaye na farko dantakarar jamiyyar PDP Abba Kabiru Yusuf kuma siriki ga injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sai da aka tafi zagaye na biyu ne shi kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kayar da dantakarar jamiyyar ta PDP Abba Kabiru Yusuf.
Gwamna Ganduje na jagorantar kwamitin binciken rikicin siyasar jihar Edo
Shekarar 2023: Mecece makomar Takai a siyasar Jahar Kano?
Jim kadan bayan rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu ne siyasar jihar Kano ta sake salo.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkiri karin masarautu hudu a jihar Kano daga masarautar Kano.
Masu sharhin al’amuran yau da kullum suna ganin yayi hakan ne domin bakantawa ‘’yan birni saboda kin zabar sa da suka yi a shekarar 2019.
Tunda Gwamna Ganduje zai kammala wa’adinsa ne a shekarar 2023 masu nazari suna ganin sanatan Kano ta arewa wato yankin da gwamna Ganduje ya fito shine tauraruwar sa take haskawa.
Masana lamuran na siyasa sun alakanta hakan ne saboda yawancin Gwamnoni dake kammala wa’adin mulkinsu na biyu suna sha’awar komawa majalisar dattijai domin a cigaba da damawa da su a siyasar kasa da ta jihar su.
Akwai Gwamnoni irin su Jonah Jang da Umaru Tanko Almakura da Kashim Shettima da Aliyu Magatakarda Wamakko da dukkansu suna majalisar dattijai.
Wasun su musanya suka yi ta kujerar Sanata da na yankunan su.
To haka ma anan Kano ake ganin Gwamna Ganduje zai iya musanyawa Sanata Barau da takarar Gwamna a jamiyyar APC domin shi ya tafi ya wakilici Kano ta Arewa a majalisar dattijai domin shi ma a cigaba da damawa dashi a siyasar jihar Kano.
Amma shima mataimakin gwamnan Kano na yanzu Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna wanda wasu suke ganin shine Goodluck Jonathan na Kano ba zai ki neman wannan Kujerar ba sakamakon yadda yake da tagomashi na siyasa.
Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna dai ya taba yin shugaban karamar hukumar Nassarawa har sau biyu a gwamnatin ANPP sannan yayi kwamishinan noma a karshen gwamnatin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Jagorancin siyasar birnin Kano: Sha’aban Sharada ko Mukhtar Ishaq Yakasai?
Sarkin Muslim ya bukaci gwamnatin tarayya samar da hanyoyin dakili matsalolin siyasa da addinai
Haka da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zama gwamna a shekarar 2015 Nasiru Gawuna ne mutum daya tilo daga tsohuwar Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso da ya sake zama kwamishina a gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje.
To amma ba’a nan gizo yake saka ba ,zaben shekarar 2023 zai banbanta da sauran zabuka inda ake ganin ‘’yan birni zasu taru a bayan nasu su zaba sakamakon raba masarauntar Kano da gwamnati tayi.
Ba kasafai gwamnoni ke san mataimakan su su gaje su a mulki ba,saboda suna ganin bijirewa daga wajen su.
Amma gogewa da yan siyasar biyu suke da shi wato Nasiru Yusuf Gawuna tare da Sanata Barau Jibril za’a goga wajen wanda jamiyyar ta APC zata tsayar takar muddin kowannen su ya nuna sha’awar sa ta zawarcin kujerar gwamnan ta jihar Kano.