Siyasa
2023 : Mambobin majalisar dokokin Kano 8 sun sauya sheƙa daga PDP zuwa NNPP
Mambobin majalisar dokoki na jihar Kano Takwas sun fice daga jami’iyyar PDP zuwa NNPP mai kayan marmari.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da mambobin majalisar suka fitar tare da ai kewa shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari.
Ta kardar ficewar da shugabanta ya karba kuma ya musu fatan Alkhairi a sauyin shekarar da sukai.
Mambobi takwas da suka sauya shekarar daga PDP zuwa NNPP sun hada da
1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja da ke wakiltar karamar hukumar Gezawa.
2.Hon. Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa.
3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.
4. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.
5. Hon. Tukur Muhd Fagge.
6. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.
7..Hon. Garba Shehu Fammar Kubiya.
8.. Hon. Abubakar Uba Galadima Bebeji.
8.. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.
Sanarwar hakan na zuwa ne dai bayan da Daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar kuma aka rabawa manama labarai a makon da muke shirin bankwana da shi.
You must be logged in to post a comment Login