Labaran Wasanni
2026 World Cup : Gianni Infantino ya gana da Donald Trump
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya tattauna da shugaban kasar Amurka Donald Trump kan batun karbar masaukin baki na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 da kasar zata yi.
Kasashen da suke mambobi a hukumar ta FIFA a shekarar 2018 ne, suka zabi kasar ta Amurka da kuri’u 134 a maimakon kasar Morocco dake da kuri’u 65.
Shugabannin sun tattauna game da gina sabowar shalkwatar hukumar kwallon kafa ta duniya a kasar, tare da sake nazartar tsare-tsaren karbar bakuncin gasar.
Gianni Infantino ya kuma ziyarci ofishin sashin kula da al’amuran shari’a na kasar ta Amurka, yana mai godiya ga sashin kan bayar da gudunmowa wajen yaki da cin hanci da rashawa a fannin kwallon kafa.
You must be logged in to post a comment Login