Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FIFA Rankings : Eagles ta matsa zuwa mataki na 29

Published

on

Najeriya ta matsa mataki na 29 a fannin kwallon kafa a fadin duniya a wani sabon jaddawali da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar.

Wannan na kunshe ne a cikin sabon jadawalin mataki na kasashen duniya da FIFA ta fitar a yau Alhamis.

FIFA dai ta saba fitar da jadawalin ne a karshen kowane wata, amma kuma an shafe kimanin watanni shida ba tare da an wallafa jadawalin ba, sakamakon bullar cutar COVID-19.

Hukumar ta ce, duba da dawowa da ci gaba da wasanni a farko wannan watan musamman a nahiyar turai, za a ci gaba ta wallafa jadawalin a duk karshen kowane watan.

A matakan da ta fitar na baya-bayan nan, kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Super Eagles ita ce ta 31, hakan ya baiwa Najeriya damar matsawa zuwa mataki na 29, inda kasar Senegal take a mataki na 20 yayin da kuma Tunisia take a mataki na 26 a duniyar kwallon kafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!