Addini
Yadda ake yi wa mamaci karatun Al’qur’ani bayan ya rasu
Daga Shamsiyya Farouk Bello
Karatun Al’kur’ani a ya yin da aka yi rasuwa na janyo cece-kucen jama’a musamman yadda wasu ke ganin karantawa mamacin kur’ani kan zamo ana samama sa rahama a gun Allah ne amma wasu na ganin baiken hakan.
Sai dai wasu mutane na ganin wannan karatun kur’anin kan zamo bidi’a ya yin da wasu ke ganin cewa yin addu’a kan zamo gata ga mammaci.
Amma wani malamin addini a nan Kano, Malam Mukhtar Umar Sharada ya bayyana cewa “Duk wanda yayi karatun al’kur’ani ya yi tawassali ga wani mamaci, to shakka babu za’a ba su ladan kuma har ma a ninka masa ladan, ya yin da agefe guda kuma Allah zai yi wa mamacin rahama”.
Haka zalika Malam Mukhtar Umar ya bayyana cewa, “Duk abinda mutum yake yi na alheri idan ya mutu, kuma makusantanshi suka dora daga nan ko cigaba da yi, shakka babu ladan zai kai gare shi”.
Ya kuma kara da cewa, duk mutumin da yake yiwa mamaci tawassali da abin alkairi, to shima zai samu maiyi masa makamanciyar wannan addu’a.
A kan hakan ne wakiliyarmu Shamsiyya Farouk Bello ta tattauna da Malam Mukhtar Umar Sharada don jin hukuncin karanta al’kur’ani ga mamaci.
You must be logged in to post a comment Login