Labarai
Mai Martaba sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar ya ce in aka yi laakari da irin cigaba da aka samu a kasar nan cikin shekaru sittin da samun ‘yan cin kai, ya zama lallai ‘yan Najeriya su dinga adu’o’in dorewar zaman lafiya a kasar nan.
Sarkin na Karaye ya bayyana hakan ne a Daren jiya alhamis yayin liyafar cin abincin dare da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a wani bangare na bikin ranar samun yancin kai.
Sarkin na Karaye ya Kara da cewa anan Kano abin alfahari ne in akayi laakari da cewar ana zaune lafiya babu tashin hankali a tsakanin al’umma.
Da yake jawabi yayin gabatar da jawabin da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce abin a godewa sarakunan masarautu biyar gaba daya ne tare jamian tsaro bisa ga yadda suke baiwa gwamnatin hadin Kai wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar nan.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa taron liyafar cin abincin daren na bikin ranar cika shekaru 60 da samun yancin Kan Nigeria ya samu halartar jamian gwamnati daga bangarori da dama
You must be logged in to post a comment Login