Labarai
Za mu samar da dabaru a guraren zubar da shara – Dr. Kabiru Getso
Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta ce za ta samar da wasu dabaru a guraren zubar da shara a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, yayin taron bitar makon muhalli na shekarar 2021 da aka gudanar.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Sunusi Kofar Na’isa ya fitar, ta ce shirin ya samu nasara matuka musamman wajen tsaftace jihar ta hanyar yashe manyan magudanan ruwa da kwashe sanannun wuraren zubar da shara.
“Mun ware mako guda don tsaftace muhalli, har ma muka kara kwanaki uku akai don bibiyar wuraren tare da tabbatar da babu wani ragowar datti a cikin al’umma” inji Kabiru Ibrahim Getso.
Dakta Getso ya kuma ce sabbin dabarun suna kan hanya musamman ma shirin gwamnati na yin yarjejeniya da wani kamfanin sarrafa shara.
“Muna da sanannun guraren zubar da shara a jihar Kano, wadanda muka yi amfani da makon muhalli wajen kwashe sharar cikin su, da suka hadar da: Kofar Wambai Kan Badala, Dorayi Gidan Sarki, Gobirawa da Naibawa ‘yan kankana, sauran su ne Rijiyar lemo ‘yan rake, Kwana shida Bonker, Yakasai ‘yan jakai da Wuju-wuju” a cewar Getso.
Dakta Kabiru Getso, ya ce, nan ba da dadewa ba jihar Kano za ta fita daga barazanar da shara ke yiwa al’umma.
You must be logged in to post a comment Login