Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamantin Kano ta rufe wani gidan mai sakamakon karya dokar tsaftar muhalli

Published

on


Gwamantin Kano ta rufe gidan mai na Aliko da ke Dakata a karamar hukumar Nasarawa tare da cin tarar su naira dubu dari biyu.

Hukuncin hakan ya biyo bayan karya dokar tsaftar muhalli da suka yi a yau.

Kwamishinan muhalli na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bai wa kotun tafi da gidan kan tsafatar muhalli umarnin zartar da hukuncin sabada karya dokar da gidan man yayi.

Haka kuma an rufe tashar mota ta Kano line tare da cin tarar su naira dubu dari biyu su ma.

Getso ya ce, ba za a bude gidan man da tashar motar ba har sai sun cika ka’idojin da ma’aikatar za ta gindaya musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!