Kiwon Lafiya
Najeriya ta shiga taswirar masu yaƙi da cutar Sanƙarau – NCDC
Cibiyar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa NCDC, ta ce Najeriya ta shiga cikin taswirar duniya wajen yaƙar cutar sanƙarau kafin shekarar 2030 kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta ƙaddamar.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban hukumar NCDC Dakta Chikwe Ihekweazu ya fitar.
Ya ce matakin ya nuna gagarumin jajircewa da ƙasar nan ke yi, na shawo kan cutar sanƙarau, musamman ganin yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa.
A cewarsa yaƙi da cutar na da matuƙar mahimmanci ga yan Najeriya, kuma yaƙi da ita babban ƙalubale ne ga lafiyar jama’a.
Ihekweazu ya kuma ce, taswirar duniya ta tsara wani shiri don magance manyan abubuwan da ke haifar da cutar sankarau, da ke haddasa mutuwar kashi 70 cikin ɗari.
You must be logged in to post a comment Login