Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Abinda ya sa likitoci suka shiga yajin aiki a Najeriya

Published

on

Gamayyar Kungiyoyin likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD ta tsunduma yajin aiki ranar Litinin, bayan wa’adin kwanaki 14 da ta bawa gwamnatin kasar ya cika.

Shugaban kungiyar a Najeriya Dakta Aliyu Sokomba a makon jiya cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce basu da zabi illa su tsunduma yajin aiki, bayan da gwamnatin Najeriya ta gaza cika sharuddan da suka gindaya.

Kungiyoyin sun ce sun shiga yajin aikin ne saboda, rashin isasshen albashi da kuma kayan kariya musamman ga likitocin da ke yaki da cutar korona.

Sama da mutum 15,000 suka kamu da cutar Covid-19 inda mutum 400 suka mutu, kamar yadda kididdigar hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta ta Najeriya wato NCDC ta bayyana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!