Kiwon Lafiya
Bikin makon likitoci: Za mu kula da lafiyar mazauna karkara – NMA
Ƙungiyar likitoci ta ƙasa NMA ta ce, za ta shiga yankunan karkara don kula da lafiyar al’ummar da ke rayuwa a cikin su.
Shugaban ƙungiyar a nan Kano Dakta Usman Ali ne ya bayyana hakan a wani ɓangare na bikin ranar likitoci da ake ci gaba da gudanarwa.
“Za mu bayar da gudunmawar da ta da ce ga al’umma musamman ma mutanen karkara domin ganin su ma ba a barsu a baya ba wajen kula da lafiyar su” inji Dr Usman Ali.
Ƙaramar hukumar Ɓagwai na cikin ƙananan hukumomin Kano da suka rabauta da samun tallafi a bikin makon, domin kuwa a wani zagaye da ƙungiyar ta yi a asibitin garin Ɓagwai ta raba magunguna kyauta da yiwa wasu aiki.
Cikin magungunan da aka raba sun haɗar da magungunan cutar zazzaɓin cizon sauro da na ciwon idanu da hawan jini da cutar ulcer da ciwon haƙori da kuma na kunne da sauran cututtukan da ke addabar mutane a kowanne ɓangare.
You must be logged in to post a comment Login