Labarai
DSS ta bankado yunkuri tayar da tarzoma bayan zabe
- DSS ta gano wani yunkurin tayar da tarzoma yayin gudanar da zabe a Nijeriya.
- Wasu mutane sun yi shirin tayar da rikici bayan kammala zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.
- Shugaban DSS Peter Afunanya ya ce ire-iren matsalolin babbar matsala ce ga damukradiya.
Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta gano wani yunkuri na tayar da tarzoma yayin da ake kara tunkarar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
A cewar hukumar ta DSS, ‘wasu mutane da ba ta kai ga bayyana sunan su ba, na shirin ta da rikici bayan kammala zaben gwamnonin jihohi, da aka shirya yi a ranar Asabar 11 ga wata, daga bisani aka mayar da shi ranar 18 ga watan Maris din bana.
A cikin sakonnin da jami’in hulda da jama’a na hukumar Peter Afunanya ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce kulle-kulle da ‘yan siyasa ke yi domin cimma burikansu na ‘kashin kai/
Haka ya kara da cewa yin hakan zai haifar da babbar matsala ga damukaradiyyar Nijeriya.
A don haka ya bayyana cewa ‘a shirye hukumar take wajen dakile ire-ien matsalolin nan a fadin kasar nan baki daya’.
Rahoton: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login