Labarai
Kungiyar Miyetta Allah ta sha alwashin daukar matakin shari’a a kan ‘yan sa-kai jihar Sokoto
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah ta sha alwashin daukar matakin shari’a a kan kungiyar ‘yan sa-kai a jihar Sokoto biyo zargin da ta yi mata na hallaka mambobin kungiyar.
Kungiyar ta Miyyeti Allah, ta ce, ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobinta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.
Shugaban kungiyar ta kasa Baba Usman Ngelzerma ya ce, wannan rikici ya barke ne tun a juma’ar da ta gabata sakamakon harin da tawagar ‘Yan sa-kan suka kai matsugunan makiyayan, lamarin da ya janyo sanadiyyar rasa rayuka da kuma kona rugagen Fulanin.
Ngelzerma ya kuma ce, daga cikin matsugunan Fulanin da aka kai wa hari sun hada da Tsola da Asara da Karan Biki da kuma Sakamaro duka a yankin Gwadabawa, kuma an jikkata mutane da dama.
Shugaban kungiyar Fulanin na kasa Baba Usman Ngelzerma ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen dakile wannan matsala da kuma hukunta duk wadanda aka samu da hannu a cikin kisa da barnatar da dukiyar mambobun kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login