Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Gwamnatin Chadi ta umarci jakadan Jamus ya fice mata daka kasa cikin kwanaki 2

Published

on

Rahotanni daga Ndjamena babban birnin kasar Chadi sun tabbatar da cewar, gwamnatin mulkin soji kasar ta umurci jakadan kasar Jamus, Jan Christian Gordon Kricher, da ya bar kasar Cikin kwanaki biyu.

A wata sanarwa da suka fitar ta bakin kakakin gwamnatin kasar, hukumomin na Chadi sun ce sun yake shawarar korar jakadan na Jamus ne saboda ba ya mutunta dokokin diflomasiyya sannan mutum ne da ke yin katsalanda ga harkokin cikin gida na kasar.

Ya zuwa yanzu jakadan na Jamus bai kai ga mayar da martani kan wannan batu, inda ba wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Kasar ya fidda kana ba wata sanarwa da aka samu daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus din.

Gabanin sallamar da aka yi wa jakadan dai, ya sha sukar hukumomin kasar kan jinkirta gudanar da zaben Shugaban Kasa da kokarin da ake yi na share wa shugaban da ke rikon kwarya, Mahmad Idriss Deby, hanya ta nema shugabancin kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!