Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu hukunta jami’an da ke karbar cin hanci- Rundunar Yan sandan Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce, za ta hukunta duk wani jami’inta da ta samu da karbar cin hanci a hannun al’umma.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Usaini Gumal, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yin holin wasu mutane da aka kama da aika laifika daban-daban a jihar.

Ya kuma ce yanzu haka rundunar ta mika mutane 426 da ke da alaka da fashin waya ga kotu, kuma tuni kotun ta aika su gidan ajiya da gyaran hali.

Kwamishinan yan sandan na Kano, ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa irin gudinmawar da suke bai wa rundunar musamman ta fusakar yakin da ta ke da yan ta’adda musamman barayin waya.

 

Rahoton; Aminu Abdu Baka Noma

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!