Labarai
Makon shayarwa- Alkhairi Orphanage ta bukaci a rika bai wa Maza Hutun Haihuwa
Ƙungiyar tallafa wa mata da marayu ta Alkhairi Orphanage and Women Development, ta buƙaci gwamnatin Tarayya da ta jihohi da su ƙara hutun shayarwa ga mata daga watanni uku zuwa shida domin bai wa mata damar shayar da jarirai yadda ya kamata.
Shugabar ƙungiyar Kwamared Ruƙayya Abdurrahman ce ta buƙaci hakan yau Litinin yayin taron faɗakar da mata masu juna biyu alfanun shayar da jarirai Nonon uwa zalla da ƙungiyar ta gudanar a Asibitin Sha ka tafi na Alkhairi Community Service da ke unguwar Garangamawa da ke nan Kano.
Kwamared Ruƙayya Abdurrahman, ta kuma buƙaci gwamnati da ta bai samar da tsarin bai wa mazan da matansu suka haihu hutu domin su samu damar tallafa wa matan musamman ta fuskar shayarwa.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiya FHI 360 a Kano Dakta Ashiru Hamza Muhammad, bayyana damuwa ya yi kan yadda wasu daga cikin kamfanoni masu zaman kansu ke hana mata da suka haihu hutun shayarwa.
Wasu daga cikin matan da suka halarci biyar da ƙungiyar ta gabatar sun bayyana jin dadinsu bisa shirya taron da kungiyar ta yi.
Sun bayyana cewa, ” Mun ji dadin wannan taro saboda an yi mana jawabai da dama musamman kan alfanun shayar da jarirai Nono zalla da kuma irin yadda ya kamata mu rika shayar da su.
Bayan tattakiN da ƙungiyar ta gudanar da safiyar yau daga unguwar Tal’udu zuwa Asibitin wanda ke a unguwar Garangamawa, Kungiyar, ta kuma yi rabon sabulai da sinadaran tsaftace tufafi ga mata masu juna biyu da suka halarci bitar.
You must be logged in to post a comment Login