Labarai
Zan shige gaba wajen samar da Gari da Tiga a Kano- Sanata Barau
Mataimakin shugaban majalisar Dattijai na Nijeriya kuma Sanatan Kano ta Arewa , Sanata Barau Jibrin ya sha alwashin yin adalci tare da taimakawa masu neman ganin an samar da jihohin Tiga da Gari daga cikin jihar Kano sun samu nasara.
Sanata Barau ya bayyana hakan ne a jiya Laraba , ya yin da Mambobin ƙungiyar fafutukar hakan ƙarkashin jagorancin Sanata Mas’ud El Jibrin Doguwa suka kai masa ziyara a Majalisar.
Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban Majalisar , Ismail Mudashir ya fitar aka rabawa manema labarai.
Ta cikin sanarwar Sanata Barau , wanda ya kasance shugaban kwamitin duba kundin tsarin mulkin ƙasar nan , ya ce ‘Majalisar zata yi duk mai yiwuwa don ganin an bawa Kowa dama a ƙasar kan abinda yake nema’.
Tun da farko dai shugaban tawagar Sanata Mas’ud El Jibrin Doguwa, ya ce ‘akwai bukatar sake samun jihohi biyu daga cikin Kano , kasancewar tsawon shekaru 40 ake ta fafutukar hakan don ganin an Samarwa da ɗumbin al’ummar jihar cigaban da ya fi na yanzu da take dashi’.
Rahoton: Aminu Halilu Tudun Wada
You must be logged in to post a comment Login