Labarai
Gobara tayi sanadiyar mutuwar mutum uku, da konewar gidajen dubu a Barno
Akalla wasu ‘yan gudun hijira uku ne suka mutu, sannan sama da gidaje 1000 suka kone bayan da gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira a Muna da ke Maiduguri a jihar Barno.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar Laraba kuma ta dauki sama da awa daya kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta.
Babban Darakta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa a Jihar Borno Dakta Barkindo Muhammad Sa’idu ne ya bayyana hakan a Maiduguri, inda ya ce kungiyar sa kai na CJTF, da jami’an tsaro da ma su kansu ‘yan gudun hijira, sun taimaka gaya wajen kashe gobarar.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login