Labarai
Tsaftar muhalli: Za mu haɗa kai da hukumar KAROTA don hana karya doka – Nasir Garo
Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano ta ce, za ta duba yiwuwar yin haɗin gwiwa da hukumar KAROTA don yaƙi da masu karya dokar tsaftar muhalli musamman ma matuƙa adaidaita sahu.
Kwamishinan muhalli na jihar Nasir Sule Garo ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan kammala duban tsaftar muhalli na ƙarshen watan Disamba.
Tsaftar muhalli: Za mu ɗauki tsatstsauran mataki kan ƴan sahu -Nasiru Garo
Garo ya ce, halayyar da matyuka adaidaita sahu suka nuna a wannan rana abin takaici ne don haka gwamnati ba za ta lamunci karya mata doka ba.
“Ba mu ji daɗin yadda masu adaidaita sahu suka fito kan tituna suna lodin fasinjoji ba, tabbas wannan halayya da suka nuna abin takaici ne kuma ba za mu zuba ido su ci gaba da yin hakan ba”.
Nasir Sule Garo ya kuma “Za mu zauna da mahukuntan hukumar KAROTA don ganin yadda za su shigo aikin don taimaka mana wajen yaƙi da karya dokokin tsaftar muhalli na ƙarshen wata, musamman wajen lura da ƴan adaidaita sahu”.
Da yake bayani kan shirin da ma’aikatar muhalli ta yi a shekarar 2024 Nasir Sule Garo ya ce, za su mayar da hankali wajen ganin jihar Kano ta za ko ta ɗaya a ɓangaren tsaftar muhalli, tare da samar da shirye-shiryen wayar da kan mutane kan muhimmancin tsaftar muhallin.
Duban tsaftar muhallin na wannan rana shi ne na ƙarshe a wannan shekara ta 2023, kuma an zagaya sassa daban daban na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login