Labarai
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta gina titi a hanyar da ta tashi daga Unguwar Maidile Kwanar gidan Kaji ta bi ta unguwannin Shekar Mai ɗaki da Bubbugaji zuwa Gidan Mairodi duk a ƙaramar hukumar Kumbotso.
Majalisar ta buƙaci hakan ne a zamanta na yau Litinin sakamakon ƙudurin da mai tsawatarwar na zauren kuma Wakilin Kumbotso Mudassir Ibrahim Zawaciki ya gabatar.
Yayin gabatar da ƙudurin, ɗan majalisar na Kumbotso, ya buƙaci haɗin kan takwarorinsa na majalisar wajen yin kira da murya ɗaya ga gwamnatin wajen gudanar da aikin hanyar.
Da yake goyon bayan ƙudurin dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gabasawa Zakariyya Abdullahi Nuhu, bayyana alfanun samar da irin waɗannan hanyoyi ya yi ta na mai cewa ya kamata gwamnatin ta gaggauta gina su.
A dai zaman na yau, ƙudurin dokar kafa cibiyar yaƙi da sha da cutuka masu yaɗuwa, da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, gabatar wa majalisar dokokin, ya tsallake karatu na ɗaya a zauren.
You must be logged in to post a comment Login