Labarai
Kashim Shettima ya bayyana kaduwa bisa rasuwar Audu Ogbeh

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya nuna kaɗuwarsa kan rasuwar tsohon ministan noma, Cif Audu Ogbeh.
Shettima ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa ta’aziyya ga iyalan marigayin ranar Litinin, inda ya ce Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin jagorori na gari.
Ya kwatanta mutuwar Ogbeh da cewa rashi ne ga ɓangaren noma da kuma cigaban Najeriya.
Shettima yace ba za a manta irin gudummawar da Audu Ogbeh ya bayar wajen bunƙasa noman abinci ba a kasar nan.
Tsohon ministan noman ya rasu ne ranar Asabar yana da shekara 78.
You must be logged in to post a comment Login